28 Nuwamba 2021 - 14:40
Iran Na Fitar Da Kayayyakin Da Ba Na Man Fetur Ba Da Ya Kai Kashi 42%

Rahotanni sun nuna cewa alkaluman da hukumar kwastom na kasar Iran ta fitar ya nuna cewa adadin kayayyakin da kasar ke fitarwa zuwa kasashe ketar da ba na dangogin man fetur ba sun kai kashi 42 cikin dari, daga wata maris zuwa nuwambar shekara ta 21 da kudinsu yakai dala biliyan 31.1

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mahdi Mir Ashrafi shugaban hukumar kula da tashoshin jirgin ruwa na Iran ya fadi cewa abubuwan da suka shafi dangogin manfetru da kasar ke fitar sun kai kashi 43 cikin dari wato kusan rabin abubuwan da iran ta fitar acikin watanni 8 sa suka gbata

Muhimman Kasashen da Iran ta fi aikewa da kayayyaki sun hada da kasar china da ya kai dala biliyan 9.1 sai kuma iraki da yawansa ya kai dala biliyan 6.1 sai kuma kasar Turkiya mai dala biliyan 3.8,

Har ila yau ya kara da cewa kayayyakin da ta aika hadaddiyar daular larabawa ya kai dala biliyan 2.9 sai kuma kasar Afghanistan maid ala biliyan 1.27.

342/